A yau Litinin ne a birnin Brussels, za’a fara shari'ar Salah Abdelsalam daya daga cikin wadanda ake zargi da kai hari kan birnin Paris, kuma shi ne kadai yake raye. An tsaurara matakan tsaro a zaman kotun wadda ta cika makil da mutane
Abdulsalam dan shekaru 28, ya bayyana a cikin farar riga kuma ba a daure ba. Ya aje gemu, jami'an tsaro masu sanye da bakaken kaya suna kewaye dashi kamar bayanan da 'yan jarida suka bayar. Ya ki ya tashi tsaye a lokacin da alkali ya umarce shi ya tashi. Ya kuma ki ya yi bayyana ko shi wane ne.
Haka nan wanda ake zarginshi tare da Abdelsalam, dan asalin kasar Tunisia, Sofien Ayari dan shekaru 24 ya halarci zaman kotun.
Zaman kotun na kwanaki hudu zai dubi harin da aka kai a watan Nuwanbar shekarar 2015 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 130 a kewaye da birnin Paris. Abdelsam ne kadai ya rayu a harin da aka ce shi ya jagoranta.
Haka ma ana kyautata zaton za’a samu bayani akan harin watan Maris din shekarar 2016 da aka kai kan tashar jiragen sama dake Burssels. ‘Yan sanda sun yi bata kashi ranar da maharan. Ana tsammanin Abdelsalam na cikin wadanda suka kai harin amma ya samu ya tsere.
Duk da haka ana sa ido sosai kan shari'ar da fatan za'a sami karin bayanai dangane da danganatakar harin da aka kai Paris, da kuma wanda aka kai a tasoshin jiragen kasa dana sama a birnin Brussels a shekarar ta 2016.
Facebook Forum