'Yan majalisun dokokin Jamhuriyar Nijar daga jam'iyyu na adawa sun yi gangami jiya talata a Birnin Konni, a matakin karshe na zagaya kasar da suka yi da nufin janyo hankulan jama'a game da wasu take-taken jam'iyyar PNDS-Tarayya mai mulkin kasar.
Shugaban wannan gangami na zagaya Jamhuriyar Nijar, Ousmana Sanda, wanda babban hadimi ne na madugun 'yan adawar Nijar, Hama Ahmadou, ya fadawa wakilin Muryar Amurka, Harouna Mamane Bako cewa, babban makasudin wannan rangadi nasu shine fadakar da jama'a game da kundin zabe sabo wanda jam'iyyar PNDS mai mulkin kasar ta fito da shi da nufin cewa idan ba dan takararta ba babu wanda zai iya lashe zabe a kasar.
Yace gamayyarsu ta 'yan adawa, ba zata yarda a yi wani abinda ya saba ma ka'ida ko ya kaucewa tsarin dimokuradiyya ba.
A nasa bangaren, Lawwali Ibrahim na jam'iyyar Hakuri, ya tabo batun kasafin kudin 2018, wanda shi ma yana daya daga cikin dalilan da suka sa 'yan majalisar fita domin zagaya kasar.
Yace nan da watanni uku zuwa hudu, 'yan Nijar zasu fuskanci tsadar rayuwa a saboda irin tanade-tanaden dake cikin kasafin kudin, yana mai cewa talaka zai dandana kudarsa. Yace kudin komai zai karu.
Sai dai kuma jam'iyyar PNDS-Tarayya mai mulkin kasar ta ce wannan gangami na 'yan adawa, ko a jikinta. Malam Abdoulkarim Ahmani yace ba yau suka saba ganin irin wannan adawar ba.
Ga cikakken rahoton Harouna Mamane Bako...
Facebook Forum