Kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya reshen Minna a jihar Neja sun yi kira taron manema labarai don bayyana nasu kiran ga membobinta don gujewa tashin hankali da tada razoma.
Sun kuma nuna muhimmancin yin zaben cikin kwanciyar hankali. Alhaji Samaila Rebe shine shugaban kungiyar reshen jihar Neja ya kuma yi kira ga mutane musamman ma matasa game da bangar siyasa.
Ya yi kiran musamman ga matasan Fulani tare da neman su gujewa shaye-shaye da bangar siyasa don kar a kaisu a baro.
Game da goyon bayan fulnai da aka ce Fulani na yi da yawun kungiyar Kautel Hore sai Rebe ya nuna cewa kungiyarsu ta Miyetti Allah daban da Kautel Hore, don haka ya fadi cewa an musu katsalandan.
Inda yace Miyetti kungiyar makiyaya ce ba kungiyar siyasa ba. Ya bayyana cewa kowa yana da ikon zabar abinda yake so a siyasance amma a daina aron bakinsu ana ci musu albasa.
Daga karshe kuma sai shugaban ya sake tabo yadda barayin shanu ke damun Fulani har ma ya bada misalin satar da aka yiwa ‘yan uwansu a kwanan nan. Ya jadda cewa Myetti Allah bata taba kutsa kai a siyasa ba.
Your browser doesn’t support HTML5