Alhaji Suleiman Danzaki tsohon shugaban kungiyar motocin sufuri ta Najeriya yayi taro da manema labarai a Abuja inda ya amsa tambayoyi kan alfanu ko rashin alfanun shigar kungiyoyin kwadago harkokin siyasa.
Hakin kowa ne a Najeriya yanzu ya shiga siyasa domin ya kubutar da kasar daga cikin halin kunci da kakanikayi da ta samu kanta.
Alhaji Danzaki yace cigaba ya kawo irin abubuwan dake faruwa. Da ana zaton idan mutum ya shiga kungiyar kwadago bai kamata yai shiga harakar siyasa ba. Ya dai iya shiga harkar noma ko wasu makamantan hakan amma ba siyasa ba. Yace amma yanzu kasar tana wayewa.Yanzu dan kwadago yana ganin abun da shugabanni keyi. Sabili da haka dole ne ya shiga siyasa koda ba zai rike katin wata jam'iyya ba.
Duk batun banbancin addini ko na bangaranci ko kabilanci zai zo ya wuce domin daga karshe abun da zai damu mutane shi ne samun shugabanci nagari. Fafitikar kungiyoyi ko na kwadago ko na siyasa ba zai hana jama'a zabar gwamnatin da suke so ba su kuma kafata. Idan gwagwarmaya tayi tsanani kungiyoyin gwadago sai su hade su fuskanci gwamnatin da basa so su kawar da ita.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.