Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Tsoron Tashin Hankali: Wasu 'Yan Najeriya Na Komawa Jihohinsu


Mutane da suke rububin tserewa zuwa jihohinsu
Mutane da suke rububin tserewa zuwa jihohinsu

Yayinda ya saura 'yan kwanaki kadan a soma zabe a Najeriya, wasu suna barin inda suke da zama suna komawa jihohinsu na asali domin gujewa tarzoma da ka biyo bayan zaben kamar yadda ya faru a shekarar 2011

Furucin wasu 'yan siyasa suna tsoratar da mutane da firgitar dasu lamarin da ya sa suka soma komawa jihohinsu.

'Yan arewacin Najeriya da ma na kudancin kasar suna komawa inda suka fito. Misali 'yan arewacin Najeriya dake zaune a yankin Niger Delta suna barin wurarensu alatilas suna komawa arewa sabili da kalamun mutanen yankin. Akwai fargabar cewa zabukan ka iya zuwa cikin tashin hankali.

Wasu da Muryar Amurka ta zanta dasu domin sanin dalilinsu na barin inda suke zama sun ce zasu koma gida saboda rikice-rikicen siyasa. Wani Magaji Maiduguri yace 'yanuwansu da suke tare dasu suna tsorata su. Yace kashi biyu cikin uku duk sun tafi.

Kasumu Hamisu yace 'yan asalin wurin da suke zama suna batun cewa za'a yi rikici a wannan zaben. Sabili da haka iyayensu sun gargadesu da su koma gida.

Haka ma wasu 'yan kudancin Njeriya da suka kwashe shekaru da dama suna zaune a arewa suna kwashe kayansu suna komawa gida domin fargabar abun da ka biyo bayan zabe kamar yadda aka yi a shekarar 2011.

Ga bayanin Lamido Abubakar Sokoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG