Cibiyar ta musamman zata kunshi wakilai daga rundunar 'Yansanda da ta Soja, da wakilan hukumar tsaron 'Yansandan farin kaya watau SSS, da hukumar kastam, da hukumar shige da fice watau Imagirashon.
Saura sun hada da hukumar Civil Defense, da kuma hukumar kiyaye hadura ta kasa.
Wannan cibiya zata kasance karkashin jagorancin kwamishinan 'yansanda na jihar Ibrahim Idris. A bayanan da suka fitar, sun ce aikin kwamitin sun hada harda sanya ido kan yadda al'amura zasu rika wakana a sassa daban daban na na jihar kano a lokutan zabe da kuma bayan an kammala zabe.
Wannan cibiya zata rika karbar bayanai ko korafe korafe daga jama'a ta woyar tarho domin daukar mataki.
Haka kuma cibiyar ta fitar da ka'idoji da jama'a zasu kiyaye daga ranar jumma'a 27 ga watan nan.
Ga karin bayani.