Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, tace ta kammala dukkan shirye shirye domin gudanar zabe ranar Asabar 28 ga wannan wata.
Shugaban hukumar zaben Farfessa Attahiru Jega ne ya bayyana haka a lokacin taron da hukumar tayi da masu ruwa da tsaki daga jam'iyun siyasa. Farfessa Jega ya yaba da nasarorin da hukumar ta samu na aikace aikacen na'urar tantance masu jefa kuri'a.
Farfessa Jega yace shi tsohon malamin makaranta ne, kuma a jarrabawa idan dalibi ya sami kashi 60 cikin dari, ai ya sami nasara a jarrabawar, saboda haka yazo da mamaki ace duk da irin wannan nasarori da na'urar ta samu wasu su dage cewa ai sai a yi watsi da ita baki daya cewa ta gaza.
Da yake magana bayan taron, Speto Janar na 'Yansandan Najeriya Suleiman Abba ya shawarci jama'a kada su tsaya bayan sun kada kuri'a domin yana cikin dokokin zabe.
Da aka nemi tabbacin 'Yansanda ba zasu fito su goyi bayan wata jam'iyya ba, baturen 'Yansanda na kasa yace sun horasda jami'na tsaron domin su kaucewa nuna son zuciya lokacin zabe.
Ga karin bayani.