Argentina ta doke Bolivia da ci 3-0 a ci gaba da wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya a yankin kudancin Amurka.
Lionel Messi ne ya ci wa Argentina duka kwallayen.
Wadannan kwallaye sun ba Messi damar zama dan wasan kudancin Amurka da ya fi yawan kwallaye.
Dan shekara 34, Messi ya ci kwallaye 79 ga kasar ta Argentina, abin da ya ba shi dama ya yi wa dan wasan Brazil Pele wanda ke da kwallaye 77 fintinkau.
Gabanin wannan wasa na Argentina, Uruguay ta lallasa Ecuador da ci daya mai ban haushi.
Hakan ya ba ta damar darewa matsayi na uku a teburin neman gurbin shiga gasar ta cin kofin duniya.
Kasashe hudu daga nahiyar da suka yi zarra, su ne za su je gasar ta cin kofin duniya.
Brazil ce a saman teburin da maki 24, Argentina a matsayi na biyu da maki 18 sai Uruguay da maki 15 baya ga Ecuador mai maki 13 da Columbia mai maki 13 ita ma.
Kasar Qatar ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarar 2022.