Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Copa America: Messi Ya Ce Rashin Kyawun Fili Ya Ragewa Argentina Tagomashi


'Yan wasan Argentina (Photo by Daniel JAYO / POOL / AFP)
'Yan wasan Argentina (Photo by Daniel JAYO / POOL / AFP)

Dan wasan Argentina, Messi ya yi korafi kan rashin “kyawun fili” a wasansu da Chile a gasar Copa America inda suka tashi da ci 1-1.

“Mun gaza samun nutsuwa. Mun kasa yin amfani da damar da muka samu, sannan ga rashin kyawun fili, idan za a fadi gaskiya.” Messi ya ce kamar yadda kamfanin dilllancin labarai na AP ya ruwaito.

Ya kara da cewa, “amma dai mun gaza samun nutsuwa sannan muna ta hanzari. Wannan kuma wani abu ne da Chile ta yi kokarin samu a lokacin da suka farke kwallon da muka ci."

"Dangane da bugun fenarti, gaskiya ban yi tsammani ya kamata a bayar ba, amma dai gaskiya ta sauya wasan baki daya.” In ji Messi.

Karawar Brazil da Venezuela
Karawar Brazil da Venezuela

A rukunin B, Neymar ya ci wa Brazil kwallo ta bugun fenarti a karawar da suka yi da Venezuela inda aka tashi da ci 3-0.

Wannan shi ne wasan farko na rukukin na B da aka buga ranar Lahadi, wanda hakan ya ba Brazil damar fara wa da kafar dama a kokarinta na kare kofin gasar da take rike da shi.

Ba a abokantaka a fili, Suarez ya fadawa Messi kan karawarsu a gasar Copa America

Ba a abokantaka a fili, Suarez ya fadawa Messi kan karawarsu a gasar Copa America
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:52 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG