Wannan dai wata sabuwar dambarwa ce da ke kokarin kawo koma baya ga sauya shekar ta Messi, wanda masu fashin baki ke ganin wani yunkuri ne na karshe na Barcelonar na hana dan wasan mai shekaru 34 komawa PSG.
Messi ya yi ban kwana da kungiyar ta Barcelona da ya kwashe tsawon shekaru 21, cikin alhini da zubar da hawaye a ranar Lahadi, a wani taron manema labarai, inda kuma aka alakanta shi da komawa PSG ta kasar Faransa.
Barcelona ta yanke shawarar barin Messi ya bar ta, bayan da ta gano cewa biyan albashinsa kan iya sabawa dokokin kashe kudade na kungiyoyi, haka kuma zai iya jefa ta a cikin mawuyacin halin tattalin arziki na tsawon shekaru 5 masu zuwa, duk kuwa da cewa dan wasan ya amince da sabon kwantaragi da kungiyar, tare kuma da rage yawan albashinsa.
Hakan ya sa nan take PSG ta kai caffa kan Messi, tare da tattaunawa da jami’ansa, inda kuma tun a ranar Lahadin aka sa ran isar Messi a birnin Paris, domin kammala shirye-shiryen komawarsa.
Sai dai kuma lauyoyin na Barcelona da suka garzaya kotu, sun gabatar da kara inda suke kalubalantar komawarsa PSG, wadda suka ce ita ma kan iya saba dokar kashe kudade ta kungiyoyi idan ta sayi Messi, saboda la’akari da yanayin da Baitul malin ta yake ciki.
A bayanin karar da lauyan Barcelona Juan Branco ya fitar, ya ce “matsalar kudade da PSG ke fuskanta a halin yanzu, ta ma fi muni akan ta Barcelona”.
A wata sabuwa kuma, kashi na neman gamewa ga kungiyar ta Barcelona, a yayin da rahotanni suka bayyana cewa sabon dan wasanta Sergio Aguero, na duba yiwuwar barin kungiyar, bayan ficewar Lionel Messi.Aguero ya koma Bacelonar ne a wannan bazarar daga Manchester City ta Ingila.
Amma jaridar wasanni ta Forbes Reports ta ruwaito cewa yanzu haka dan wasan na neman hanyar warewa.
Yanzu haka kuma dan wasan ya shiga hutun rauni da ya samu har na tsawon makwanni 10 ba tare da ya buga kwallo ba.
Kungiyar ta fitar da sanarwa cewa gwajin da aka yi masa ya tabbatar da cewa ya ji rauni kuma zai tafi jiyya ta makwanni 10.
Wata kafar watsa labarai ta Catalan mai suna Beteve, ta ba da rahoton cewa wannan dambarwa da ke addabar Barcelona kan iya kazancewa, a yayin da tuni Aguero ya sanar da lauyoyinsa da su duba yiwuwar soke kwantaraginsa da kungiyar.