Da yake jawabi wurin taron da wata kungiyar kasa da kasa dake sa ido kan fararen hula lokacin tarzoma, wato civilian in conflicts ta shirya a Abuja, wani babban hafsa a rundunar sojin Najeriya Manjo Janar Ibrahim manu Yusuf, wanda tsohon babban kwamandan runduna ta bakwai ne da ke fafatawa da Boko Haram, ya ce mayakan kungiyar su kanyi garkuwa da fararen hula ne don amfani dasu a matsayin bayi, ko suke dafa masu abinci, sannan wani lokaci sukan yi amfani dasu a matsayin kandagarki.
Janaral Manu ya ce a duk lokacin da sojojin Najeriya zasu kai farmaki, sukanyi amfani da amsa kuwa don suyi shela ga fararen hular da ‘yan ta'addan ke rike dasu su gaya masu hanyoyin da zasu bi don su kai ga tudun mun tsira, amma kasancewar Boko Haram sun sauya masu tunani inda suke gaya masu cewa in suka fito sojoji zasu kashesu, hakan yana sawa suna kin fiotowa.
Daga watan Janairun wannan shekara zuwa 15 ga watan Mayu rundunar sojin ta kubutar da fararen hular da Boko Haram ta yi garkuwa dasu sama da dubu uku. kuma wannan bai hada da wadanda aka kubutar lokacin hare-haren da ake kaiwa Boko Haram ba.
Da yake yiwa Muryar Amurka ‘karin bayanin abubuwan da wadanda aka kubutar din suka fi bukata bayan kubutar dasu din, wani likita dake aikin tallafawa ‘yan gudun hijira Dakta Saleh Abba, ya ce abu na farko da ya fi kowanne mahimmanci a garesu shine kwanciyar hankali, su zauna lami lafiya ba tare da taraddadin ko za a tayar masu da bom ba a inda suke fakewa, sannan sai abinci dakuma ilmi sannan a yi batun sanao'i.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5