Me Kakaki Aminu Tambuwal Ya Sani Ne Game Da Rigimar PDP?

Kakaki Aminu Waziri Tambuwal ya zanta da Muryar Amurka.

A ziyarar da ya kowawa Muryar Amurka, sashen Hausa ya tattauna da Honorable Aminu Waziri Tambuwal, kakakin Majalisar Wakilai ta Najeriya akan zuwanshi nan Amurka, da matsalolin jam’iyyar PDP.
“Mun zo ziyarar aiki tare da ‘yan uwana ‘yan Majalisa, da kuma gabatar da wasu kasidu a jami’ar John Hopkins, da kuma cibiyar nazarin dangantakar kasashen waje ta Amurka,” a cewar Hon. Tambuwal.

Mr. Tambuwal ya cigaba da cewa “Kasidun da muka gabatar sun shafi matsalolin shugabanci a cikin kasashe masu tasowa, wanda na gabatar a cibiyar hulda ta kasashen waje ta Amurka, inda muka yi magana akan matsalolin tsaro a Najeriya, da kuma yankin yammacin Afirka.”

Dan shekaru 47 da haihuwa ya bayanna matsalolin Najeriya ta kwatantata, da sauran kasashen Afirka masu tasowa, inda ya bayanna cewa da yawa daga cikin shugabannin da ake zaba, mancewa suke yi da talakawa.

Da Salihu Garba na Muryar Amurka ya tambaye shi game da rigingimun siyasa dake barazanar tarwatsa jam’iyyar PDP, wadda shi Tambuwal din ke ciki.

“Iya sani na abunda ya kawo wannan kace nace, da rabuwar jam’iyyar PDP gida biyu, a yanzu a Najeriya shine rashin kyakkyawar shugabanci. Rashin a zauna a saurari mutane, a bude tsari na jam’iyya, a baiwa jama’a dama, kowa ya taho ya gabatar da korafe-korafensa idan yana da su, a saurare shi a dauki mataki, a kyautata jam’iyya, a ga yadda za’a iya tabbatar da cewa kowa an tafi tare da shi.

Your browser doesn’t support HTML5

Me Kakaki Aminu Tambuwal Ya Sani Akan Rigingimun PDP - 4:04