Chief Olusegun Obasanjo tare da Janaral Ibrahim Babangida da wasu tsofofin shugabannin jam'iyyar sun gana da Bamanga Tukur da bangarensa da Kawu Baraje da nasa bangaren. To saidai bisa ga alamu kowa na kan bakarsa. Yayin da Bamanga Tukur ke ikirarin shi ne halartaccen shugaban jam'iyyar su kuwa bangaren Kawu Baraje cewa suke dan kama karya ne.
Gwamna Sule Lamido ya ce suna nan kan inda suka tsaya kuma batun wai zasu rasa kujerunsu bai ma taso ba. Ya ce bangaren Bamanga Tukur na karya ka'idodi da yin mulkin kama karya. Idan ba zasu gyara ba su sai sun gyara. Ya ce jam'iyyarsu ta PDP na nan daram. Su 'yan a kawo gyara ne kuma dole sai sun yi gyaran. Ya ce maganar za'a kaisu kotu ko za'a ciresu daga mukamansu duk burga ce su kuma sun fi karfin a yi masu burga. Ya ce babu yadda za'a yi don son zuciyar wani ko son wani a ce an mayardasu yaran wani. Idan an bi ka'idar jam'iyyar babu karya tsari babu neman farantawa wani ko ta halin kaka sai a yi tafiya tare.Amma a rusa wannan a kulla wancan a yi anfani da EFCC domin kutuntawa wasu ba zata yiwu ba.
Mataimakin shugaban jam'iyyar a arewa maso yamma Ambassador Ibrahim Kazaure ya ce babu gudu babu ja da baya sai an biya masu bukatunsu. Ya ce su ne suke da sinadarin kada PDP idan kuma an ki zasu yi anfani da shi.
Nasiru Adamu El-Hikaya nada rahoto