Bayan taro da gwamnoni a buye da ya yi a cikin fadarsa shugaba Jonathan ya fito da Tony Anenih na kwamitin amintattu a gefensa da gwamna Aliyu na jihar Neja a wani gefen na shugaban. Gwamna Babangida Aliyu ya karanta sakamakon taron wanda aka rubuta da hannu. Cikin takardar da ya karanta an umurci duk bangarorin biyu su dakatar da caccakar juna har a kai ga warware takaddamar. Ya ce zasu sake zama ranar bakwai ga watan gobe.
To saidai shugaban sabuwar PDP Kawu Baraje ya kira shugaba Jonathan da ya bude masu ofishinsu da yasa 'yansanda suka kulle a birnin Abuja. Wasu 'yan PDP irin su Aminu Dan Arewa yana ganin PDP ba zata kai labari ba muddin ta ki biyan bukatun gwamnonin nan bakwai saboda tasirinsu a siyasa. Ya yi misali da Sule Lamido wanda ya yi NEPU da PRP a ce ba za'a dama da shi ba. Duk wanda ya yi hakan nan ya tabu. Ya ce yau ka shiga Kano ka ce zaka kwaceta a hannun Kwankwaso wannan babban kuskure ne. A nashi harsashen duk gwamnonin nan bakwai babu na yarwa a harkokin siyasar Najeriya idan mutum na son ya kai labari gida.
Saleh Shehu Ashaka nada karin bayani.