Yanzu dai a fili take cewa jam'iyyar PDP ta dare gida biyu wanda ya soma da fitar gwamnoni bakwai daga zauren taron jam'iyyar. Yanzu wasu 'yan majalisar wakilai da 'yan majalisar dattawa da wasu na johohi da wasu jigajigan jam'iyyar duk sun koma sabuwar.
Ganin yadda 'yan neman canji a jam'iyyar ke yaba ma wadanda suka fice suka kafa sabuwar PDP, Bamanga Tukur ya ce wadanda suka kafa sabuwar PDP tamkar sun bar mukamansu ne kuma ya zama wajibi 'yansanda su fatartakesu. Ya bukaci 'yansanda su saka kafar wando daya da 'yan sabuwar PDP. To tun ba'a yi nisa ba 'yansanda sun soma daukan matakan nuna tasirin bukatar.
Tun lokacin da Bamanga Tukur ya hau mukamin shugabancin jam'iyyar aka zargeshi da kokarin ba Jonathan tikitin ta zarce a zabe mai zuwa na 2015. Haka ma an zargeshi da son dora dansa kan kujerar gwamnan Adamawa.Kodayake Bamanga ya musanta ba Jonathan tikitin ta zarce amma ya ce babu laifi idan dansa ya tsaya takarar neman gwamnan Adamawa.
To sai dai gwamna Sule Lamido ya zargi Bamanga da wuce gona da iri. Ya ce an zo taron kasa na jam'iyyarsu amma Bamanga ya sa an hana wani gwamna shiga taron da mutanensa kana kuma ana sake sunaye domin a shigar da mukarabansa. Bugu da kari wadanda kotu ta dakatar domin yadda aka zabesu da an ce su dawo su tsaya takara amma Bamanga ya dawo da wasu wasu kuma ya hana.
Ana wannan dambarway sai gashi shugaban kwamitin amintatu na jam'iyyar Tony Anenih ya ce Jonathan ya fito neman takarar sake tsayawa zabe. Wannan tamkar sun fita daga karamin rikici ne zuwa wani babba.
Ga karin bayani.