Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Gwamnoni 7 Dake Tawaye A PDP Suke Ciki?


Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso
Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso

Duk da cewa Muryar Amurka bashi da tabbacin inda dukkaninsu suke, amma daya daga cikin gwamnonin 7 da suka balle daga shugabancin Bamanga Tukur a karkashin jam’iyyar PDP, gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso yana kan hanyarshi ta komawa gida daga kasashen Chana da Hadaddiyar Daular Larabawa (U.A.E), da aka fi kira da Dubai.

Bello Habeeb Galadanchi na Muryar Amurka ya tuntubi gwamnan domin jin ko mene ne ya fitar dashi daga Najeriya, a dai-dai wannan lokaci.

Gwamnan yace “Ran 6 ga watan 9 na 2013 muka taho daga Kano, muka je Legas sannan muka bi ta Dubai, sannan ranar Asabar muka sauka a birnin Beijing, shedkwatar kasar Chana. Daga nan hallarci wani babban taro na duniya baki daya, na zuba jari da kasuwanci. Saboda wannan taron ne yasa muka dauki shugaban hukumar kasuwanci ta Kano, Umar Dan Sulaika, da kuma shugaban kasuwar Sabon Gari da kuma Alhaji Karami Isyaka Rabiu, domin su wakilci bangaren ‘yan kasuwan Kano.”

Gwamnan ya bayanna yadda shi da shuwagabannin kasuwancin na Kano suka zaga inda suka ga abubuwa daban-daban masu alaqa da bunkasa cinikayya da kasuwanci, sannan sun tattauna da ‘yan kasuwa masu sha’awar zuwa jihar Kano domin hada-hadar kasuwanci.

“A birnin Beijing, mun hallarci tarurruka da yawa inda muka ziyarci kamfanoni musamman wadanda suke yi mana ayyuka a jihar Kano, da wadanda suke shirin yi mana ayyuka.” A cewar Mr. Kwankwaso.

Ziyarar ta Gwamnan mai shekaru 47 da haihuwa ta bada damar ganawa da kamfanoni kamar CCECC ( China Civil Engineering Construction Corporation) wadanda suke ayyuka na jirgin kasa a cikin birane, da kuma uwar kamfanin dake gina gada a kofar Nasarawa, kuma shine yake aiki a unguwar Jakara dake cikin birnin Kano, da aka saka wa suna “Wuji-wuji” way, da kuma hanya daga Kano zuwa Zariya.

A cewar Gwamnan, tattaunawar ta bada himma ne akan yadda za’a kammala ayyukan da ake yi yanzu akan lokaci, kafin shekara ta 2015.

Gwamnan jihar Kanon, yayi wa’adin na farko a daga shekara ta 1999 zuwa 2003, kafin Malam Ibrahim Shekarau a karkashin jam’iyyar ANPP ya karbe ragamar mulkin. A shekara ta 2011, yayi nasarar dawowa kan kujerar mulki inda ya kaddamar da ayyuka kamar Gada a kusa da Kofar Nassarawa, da amfani da jar hula wajen wanzar da manufofinsa da akidu wadanda suka shafi aiki, da da’a da hadin kai.

Sai dai wannan tafiya da yayi ta zone a lokaci daya da rigigimun siyasa a cikin jam’iyyarshi, mai mulkin Najeriya wato PDP. Yana daya daga cikin gwamnoni da suka balle, domin komawa karkashin shugabancin Kawu Baraje, da yin adawa da yadda Bamanga Tukur yake tafiyar da harkokin jam’iyyar.

A dai-dai lokacin da Gwamnoni kamar na jihar Ribas, Rotimi Ameachi yake fama da jami’an tsaro, inda suka hana shi shiga gidan Gwamnati, shi ko Dr. Kwankwaso yana kan hanya domin gudanar da wasu harkokin jihar. Da Muryar Amurka ya tambaye shi ko me ake ciki a halin yanzu, dan sabuwar PDP din yace sai ya koma Kano tukunna, kafin ya iya fadin wani, domin tabbatar da halin da ake ciki.

Masu magana suka ce “idan makaho yace a yi wasan jifa, to ya san ko me ya taka”.

Ga hirar Gwamnan da Bello Habeeb Galadanchi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:34 0:00
Shiga Kai Tsaye
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG