Mbappe Zai Bar Paris Saint- Germain

Yayin da Mbappe yake jawabi kan shirinsa na barin PSG INSTAGRAM/@k.mbappe a ranar 10 ga watan May, 2024,

Shekara bakwai Mbappe ya kwashe yana bugawa PSG wasa, inda ya zura kwallaye 255 amma bai kai ga lashe kofin zakarun turai ba.

Dan wasan kwallon kafar kungiyar PSG Kyliaan Mbappe ya sanar da shirinsa na barin kungiyar ta Paris Saint Germin da ke Faransa.

Ana ta hasashen Mbappe zai koma kungiyar Real Madrid ne a wasan kaka mai zuwa.

A wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafin X, Mbappe ya ce wasan da zai bugawa PSG a ranar Lahadi da za su kara da Toulous shi zai zamanto wasansa na karshe da zai buga a gida.

“PSG kungiya ce da ba zan manta a rayuwata ba. Zan fadawa kowa cewa na samu damar buga kwallo a wannan kungiya.” Mbappe ya ce cikin tattausar murya.

Shekara bakwai Mbappe ya kwashe yana bugawa PSG wasa, inda ya zura kwallaye 255 amma bai kai ga lashe kofin zakarun turai ba.