Ana ci gaba da gudanar da zanga zangar kin jinin harin da Rasha ta kai a kan Ukraine a manyan birnen Amurka da dama, inda masu zanga zangar ke kira ga shugaban Rasha Vladmir Putin ya tsagaita hadarin makamai masu lizzami da kisan da sojojin Rasha ke yi.
Duk da yanayi mai tsananin sanyi, daruruwan mutane sun yi tattaki a gundumar Manhattan ta birnin New York zuwa ofishin jakadancin Rashan a Majamisar Dinkin Duniya, inda wasu suka yafa tutocin Ukraine suna wake wake suna kira da a kawo karshen zubda jini.
Birnin shine birnin dake dauke da ‘yan kasar Ukraine fiye da ko ina a Amurka.
Masu zanga zangar da galibinsu ‘yan kasar Ukraine ne, sun rike kwalaye masu dauke da rubuta kamar haka, “A hana Putin a dakatar da yakin,” “ku cewa Putin ah’a,” “Ku hana Putin ku ceci Ukraine,” “Putin dauke hannunka a kan Ukraine” da sauran su.
Mutane da dama sun bayyana damuwar da suka shiga sakamakon wannan mamayar da Rasha ta kaiwa Ukraine. Daya daga cikin masu zanga zangar da Muryar Amurka ta yi hira da ita ta ce "abin damuwa ina kallo ana kaiwa kasa ta hari ana kashe fararen hula da tsofaffi dama kowa da kowa”.
Wata kuma da Muryar Amurka ta yi hira da ita, ta buge da kuka tana cewa “wannan ba batu ne na Ukraine kadai, abu ne da ya shafe kowa saboda barnar da ake yiwa iyalai”.
Sai dai akwai wadanda suka shiga zanga zangar da ba ‘yan Ukraine bane. Daya Wata mace tace, "ni ‘yar Rasha ce kuma na ji matukar kunya da abin da kasa ta ke yi a Ukraine, na ji kunya, abin da ake yi bai dace ba”.
A jiya Jumma'a, masu zanga zanga suka yi cincirindu a dandalin Times Square a tsakiyar gundumar Manhattan a nan New York domin kalubalantar harin da Rasha ta kaiwa Ukraine, inda tuni aka kashe sama da sojojin Ukraine 130.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5