Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Atiku Ya Nemi Gwamnati Ta Kwaso ‘Yan Najeriya Da Ke Ukraine


Atiku Abubakar (Instagram/ Atiku Abubakar)
Atiku Abubakar (Instagram/ Atiku Abubakar)

“Ina so na yi kira ga gwamnatin Najeriya, da ta yi iya bakin kokarinta wajen kwaso ‘yan kasarta, wadanda akasarinsu dalibai ne.” Atiku ya ce.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi kira ga hukumomin Najeriya da su kwaso ‘yan kasar da ke zaune a Ukraine.

Kiran na Atiku na zuwa ne sa’o’i bayan da Rasha ta kai mamaya kasar ta Ukraine, inda dakarun Shugaba Vladimir Putin suka kai hare-hare kan wasu muhimman birane ciki har da Kyiv babban birnin kasar.

“Ina so na yi kira ga gwamnatin Najeriya, da ta yi iya bakin kokarinta wajen kwaso ‘yan kasarta, wadanda akasarinsu dalibai ne.” Atiku ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.

Atiku ya kuma yi kira ga bangarorin da ke wannan takaddama, da su rungumi hanyar diflomasiyya wajen warware sabanin da ke tsakaninsu.

“Wannan rikici tsakanin Rasha da Ukraine na bukatar dukkan kasashe su tashi tsaye su rungumi hanyar diflomasiyya, don kwantar da wannan tarzoma.” Atiku ya kara da cewa.

Sai dai cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin Najeriya ya fitar wacce shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje ta wallafa a Twitter, Abike Dabiri-Erewa, ta ce duk dan Najeriyar da ya ga wannan al’amari zai tayar mai da hankali, ya nemi mafaka a wurin da zai kasance babu hadari.

“Amma kowa ya tabbata ya sabunta takardunsa, don ya samu saukin dawowa idan al’amura sun inganta.” Sanarwar ta ce.

Ko da yake, wasu rahotonni sun ruwaito Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffery Oyeama yana cewa, da zarar an bude filayen jiragen kasar, za su fara kwashe 'yan Najeriya da ke sun ficewa daga kasar.

An jima ana kai ruwa rana tsakanin Rasha da Ukraine tun bayan da Putin ya jibge dakaru sama da dubu 150 a kan iyakar Ukraine, matakin da Amurka da sauran kasashen yammacin duniya suka yi Allah wadai da shi.

Da ma dai Amurka da kawayenta musamman na kungiyar tsaro ta NATO sun jima suna gargadin cewa Putin na shirin mamaye Ukraine, batun da ya jima yana musantawa.

Matakin mamayar ya sa Amurka da wasu kasashen duniya masu fada a ji sun kakaba takunkumi karya tattalin arzikin kasar ta Rashar.

XS
SM
MD
LG