Mazauna jihar Florida a Amurka suna can auna girman ta’adin da guguwar Milton ta yi, wacce ta haddasa ruwan sama mai tsanani da ambaliyar ruwa.
Guguwar har ila yau ta haifar da iska mai tsananin gaske, kuma ta haddasa katsewar wutar lantarki a fadin yankin da ta sauka.
Kazalika ta lalata gidaje kuma ta kashe akalla mutum biyar tare da barin mutane miliyan uku ba wutar lantarki kafin daga bisani ta koma Tekun Atlantika.
Kamfanonin samar da wutar lantarki sun gargadi mutane cewa katsewar wutar na iya daukar tsawon lokaci kafin a gyara.
Guguwar ta fara ne a daren Laraba kusa da Siesta Key a gundumar Sarasota a matsayin guguwar iska mai karfin mataki na 3 tare da iska mai gudun kilomita 205 a kowace awa.