Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: Guguwar Milton Ta Sauka A Jihar Florida


Guguwar Milton a Florida
Guguwar Milton a Florida

An yi gargadin yiwuwar samun ambaliya a daren Laraba ga kusan dukkan gabar yammacin yankin Florida, wanda ya kai tsawon kilomita 500.

Guguwar Milton ta afka wa gabar tekun Gulf ta Florida a kudu da Tampa a daren Laraba, tana lalata wutar lantarki tare da zubar da ruwan sama kamar da bakin kwarya, iska mai karfi da ambaliya mai barazana ga rayuwa a sassa na tsakiya da kudu maso yammacin Florida.

Lokacin da guguwar ta sauka a kusa da Siesta Key a karamar hukumar Sarasota, Milton tana a matsayin guguwa mai matakin 3 tare da iskar da ke gudun 205 kph (120 mph), in ji Cibiyar Kula da Guguwa ta Kasa da ke Miami.

Idon guguwar ta Milton ya afka kilomita 108 kudu da Tampa, amma guguwar ta kawo ambaliyar ruwa – ruwan da ya shiga daga bakin teku zuwa cikin yankunan kasa – zuwa biranen Tampa, St. Petersburg, Sarasota da Fort Myers.

An yi gargadin yiwuwar samun ambaliya a daren Laraba ga kusan dukkan gabar yammacin yankin Florida, wanda ya kai tsawon kilomita 500.

Fiye da mutum miliyan 1 da kamfanoni suka rasa wutar lantarki, musamman a kananan hukumomin Sarasota da Manatee, in ji kamfanin dillancin labarai na Associated Press.

Hukumar ta fitar da fiye da gargadi 50 na guguwar iska har zuwa ranar Laraba rana.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG