Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Ya Dage Ziyarar Da Zai Kai Jamus, Angola Saboda Guguwar Milton


Yadda mutane ke kafe tagogi da kafofin gidajensu a wani mataki na tare karfin guguwar a jihar Florida
Yadda mutane ke kafe tagogi da kafofin gidajensu a wani mataki na tare karfin guguwar a jihar Florida

Biden ya yi alkawarin kai ziyara nahiyar Afirka yayin wa’adin mulkinsa, wanda zai kare a watan Janairu.

Shugaba Joe Biden ya dage ziyarar da aka tsara zai kai kasashen Jamus da Angola don ya zauna a Fadar White House ya sa ido kan guguwar Milton.

Ana fargabar mahaukaciyar guguwar za ta taso daga kan gabar tekun Gulf ta Florida.

Biden ya sanar da sauyin tsare-tsaren a ranar Talata, yana cewa wannan ba shi ne lokaci mafi kyau gare shi don fita daga Amurka ba.

An shirya Biden zai tashi zuwa Jamus a ranar Alhamis.

Biden ya yi alkawarin zai kai ziyara nahiyar Afirka yayin wa’adin mulkinsa, wanda zai kare a watan Janairu.

Ya kara da cewa har yanzu yana da burin kai wannan ziyara a nahiyar.

Guguwar Milton ta raunana kadan a ranar Talata, amma ta kasance wata guguwa mai karfi da za ta iya kai mummunan farmaki da ba a taba gani ba cikin karni a yankin Tampa Bay mai yawan jama'a.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG