An shiga turka-turka saboda albashi. Yayin da gwamnonin jahohi ke kare aniyarsu ta kin biyan Naira dubu 18 a matsayin albashi mafi karanci, su kuma kungiyoyin NLC da PDP da APC cewa su ke hakan zai saba ma doka.
WASHINGTON, D.C. —
Kungiyar Kwadagon Najeriya (NLC) ta fito karara ta na kalubalantar duk wani gwamnan jaha da ya ce ba zai iya biyan Naira dubu 18 a matsayin mafi karancin albashi ba.
Wannan matsayin na kungiyar kwadago na samun goyon bayan wasu ‘yan siyasa, wadanda ke cewa matsayin na gwamnoni jahohi cike yak e da rashin tausayi da aldalci.
Mataimakin Sakatare-Janar na kungiyar ta NLC, Kwamrad Nuhu Toro ya ce doka ce ta tanaji biyan Naira dubu 18 a matsayin mafi karanci na albashin don haka wajibi ne a kalubalanci matsayin gwamnonin.
Ga wakilnmu na Bauchi Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5