Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kogi: Ana Zaman Makokin Kwanaki Bakwai


Gwamnmatin jihar Kogi ta ware kwanaki bakwai domin jimamin rasuwar gwamnan farar hula na farko a jihar, Yerima Abubakar Audu, wanda shine dan takarar jam’iyyar APC zaben jihar da aka gudanar a karshen makon da ya gabata.

Yerima Audu ya rasu ne jiya Lahadi a garinsa na Ogbonicha, bayan fama da ya yi da wata ‘yar gajeruwar rashin lafiya yayin da ake kidayar kuri'u.

Dan takarar na APC na karawa ne da gwamna mai ci, Idris Wada, wanda ya ke takara a karkashin jam’iyyar PDP.

Sakamakon farko na kuri’un da aka kada na nuni da cewa, Yerima Audu ne ke kan gaba.

Gwamna Idris, ya ce ya kadu matuka da wannan rashi da jihar ta yi, yana mai jaddada cewa za a tuna da marigayin da irin gudunmuwar da ya bayar a lokacin da ya mulki jihar a shekarun baya.

Yanzu haka dai an shiga zaman jimami a jihar yayin da har ya zuwa wallafa wannan labari ba a bayyana takamaiman abinda ya haddasa mutuwar ta shi ba.

Masana da dama na ta tofa albarkacin bakinsu game da yadda wannan zabe zai kaya yayin da hukumar zabe ta INEC da ita kanta jam’iyar ta APC suka bayyana cewa sun na nazarin wannan lamari kafin a san matakin da za a dauka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:21 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG