Mutumin mai suna Tochukwu Harris Uba, ana zarginsa ne da fitar da wata kwantena dauke da haramtattun kwowayi da nauyin su ya kai kilo 576 zuwa kasar Afrika ta Kudu.
Rahotani sun ce an kama kwayoyin ne a tashar jiragen ruwa na Apapa da ke Legas yayin da ake kokarin aunasu zuwa birnin Durban na Afrika ta Kudu.
“Daya daga cikin masu laifin da aka kama din, an samu labarin cewa yana zuwa daga Enugu, sai muka tsare shi a filin jirgin sama, muka kuma yi nasarar kama shi.” In ji shugaban hukumar ta NDLEA, Alhaji Ahmadu Giade, a wata hira da ya yi wakilin Muryar Amurka, Babangida Jibril ta wayar tarho.
Wannan kamu na zuwa ne kasa da mako guda bayan da hukumar ta NDLEA ta kaddamar da wani shiri na fadarkar da kan matasa kan ayyukan hukumar da kuma illar shan miyagun kwayoyi.
Saurari wannan rahoto domin karin bayani kan wannan lamari: