Bayan da hukumomi suka tabbatar da mutuwar Yerima Abubakar Audu, dan takarar Gwamna na jihar Kogi, karkashin tutar jam'iyyar APC mai mulkin kasar, yanzu abunda ya rage shine sanin mataki na gaba da hukumar zabe zata dauka.
A hira da Sashen Hausa na Muriyar Amurka, masanain shari'a, kuma malami a sashen horasda lauyoyi a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zari'a, Barrister Bello Ibrahim Jahun, ya ce tsarin mulki bai yi wani tanadi kan yadda za'a yi idan dan takarar Gwamna ya mutu kamin a gama zabe ba, shigen abunda ya faru a jahar Kogi.
Ya ce akwai bukatar hukumar zabe ta fito da matsaya kan yadda za ta kammala wannan zabe.
Ga karin bayani.