Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Motar Shanu Ta Halaka Mutane Uku a Benue


Policemen stand guards at a burnout truck following an attacked by Boko haram militants near an Air force base in Maiduguri, December 2. 2013.
Policemen stand guards at a burnout truck following an attacked by Boko haram militants near an Air force base in Maiduguri, December 2. 2013.

Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu cikinsu har da wata ‘yar jaririya ‘yar kasa da shekara daya da rabi bayan da wata doguwar mota makare da shanu ta fadi akan wasu motoci biyu.

Doguwar motar na kan hanyar ta ne ta zuwa garin Mubi na jihar Adamawa a lokacin da hadarin ya faru.

Rahotanni sun ce hadarin ya auku ne lokacin da birikinta ya tsinke a kauyen Vinikilang da ke gab gadar jihar Benue.

Bayanai kuma sun ce akalla mutane bakwai ne suka raunata.

Wadanda suka shida lamarin sun ce sai da ya dauki tsawon sa’a daya da rabi kafin jami’an hukumar kiyaye hadurra ta tarayya tare da taimakon kauyawan su daga tirailar kana aka ceto wadanda ke cikin motocin.

Hadarin mota, na daga cikin jerin ababan da ke haifar da asarar rayuka a Najeriya saboda rashin kyawun hanyoyi ko kuma rashin motocin ingantattu.

Domin jin karin bayani, saurari wannan rahoto da wakilin mu Sanusi Adamu, ya aiko mana bayan ziyartar wurin da hadarin ya auku:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG