Shin ko mai yasa sai yanzu irin wadannan bayanai suke fitowa, tambayar da Muryar Amurka ta yiwa Farfesa Buba Namaiwa mai fashin baki kan akan harkokin tsaro da siyasa na jami’ar Anti Diop a kasar Senegal.
Farfesa yace amsami cigaban samun masu bincike ne a yanzu, idan aka duba a baya yadda ake dari-dari da zuwa a bincika ko a yake ‘yan ta’addar, amma yanzu a lamari ya canza ana ganin cewa ‘yan kungiyar Boko Haram na iya miki kansu suyi saranda ga jami’ai.
Dan gane da yanayin tsaro kuwa a jamhuriyar Nijar shine ana zargin yawancin duk wadanda ke yin wata kungiyar farar hula da cewa suna da alaka da kungiyayoyin ta’addanci, kokuma suna neman kawo tarzoma. Da alamu dai Nijar bata bin dokokin dimokaradiyya, kasancewar duk wani abu da ya faru a kasar mutum bashi da ikon fitowa domin yin Allah wadai da abin.
Your browser doesn’t support HTML5