Tuni dai aka fara ranbada wa birnin kwalliya da tutar Najeriya mai launin kore fari da kore a wasu manyan titunan birnin haka kua ma'aikatar raya babban birnin tarayya tana ta tsabtae tare tsara yanayin Abuja manyan fitullin titunan dake manyan tituna wadanda a baya basa aiki yanzu an gyaggyara su kwarai abin gwanin shaawa da yake bikin anan Abuja za ayi shi kuma ba yan Najeriya ne duka zasu iya halarta ba shugaban kungiyar yan jarida ta NUJ Mallam Garba Mohammed yace yan Najeriya su sha kurmin su.
‘’Yan jarida zasu gudanar da ayyukan su kamar yadda ya kamata kamar yadda kundin tsari ya zayyana kuma kamar yadda mutane suke tunane, duk abubuwa da yakamata suyi na shirye-shirye a matsayin jihohi da gwamnatin tarayya sun riga sunyi, wadanda ke bukatar takardan shaidar izni a lokacin da za a gudanar da rantsuwa a matakin jihohi wato shine wanda ake kira accreditation na gwamnatin tarayya ma ana nan ana ta tantancewa a tabbatar da cewa an bada wadannan takardan sabo da ita kadai ce zata iya cewa an amince kaje wajen nan da za a gudanar da wannan rantsuwa’’
Suma yan siyasa na nan nata zumudin zuwa wannan rana gama abinda Alhaji Sabo Imam ke cewa.
‘’Alhamdulillahi muna cikin farin ciki da godiya ga ALLAH sakamakon adawa da muka yi ta shekaru 16 domin tun 1999 muke tafiyar adawa to amma ALLAH bai ba Janar Muhammadu nasara ba sai a wannan karon yaba janar Muhammadu Buhari nasara cikin jamiyyar APCmu muna cikin farin ciki domin mu yan halattatun yan jamiyyar APC ne domin bamu taba yin PDP ba, adawa muke yi bana ALLAH ya kawo canji muna muna shiri mutanen mu su zo mu basu masauki a dafa abinci aci kaji a sha five alive’’
Bugu da kari tuni birnin ya fara cika yana batsewa ganin yadda mutane ke kwararowa daga sassa daban-daban na kasar kai kace sune za a rantsar a wannan ranar gama wasu dana iske sakatariyar jamiyyar APC na kasa.
‘’Sunana Bulama Galadima dagona’’
Daga ina kake?
‘’Ni dan jihar Yobe ne”
Menene ya kawo ka Abuja?
‘’Munzo nan cikin birnin tarayya domin shirye-shiryen rantsad da mai girma Janar Muhammadu Buhari’’
Alhaji Bulama a kasar nan ana fama da matsalar man fetur wanda yakai ma daga gida zuwa ofis ma yana ba mutane wahala amma kai kayo tafiya daga jihar Yobe zuwa nan Abuja don wannan rantsarwa din a can ba wahalan mai ne?
‘’Duk Najeriya ne wahalan mai amma sabo da kishin canjin da aka samu duk dan Najeriyan da yake da kishin canjin da aka samu musammam yadda aka canza wannan gwamnatin kamata yayi ya nuna farin cikin sa’’.
Sunana Mohammed Jibrin Karasuwa.
Mallam Mohammed Jibrin Karasuwa, kaima daga jihar Yoben kake ?
‘’Kwrai da gaske daga jihar Yobe nake nazo ne don nuna farin ciki na game da wannan nasarar da muka yi na jamiyyar mu ta APC wallahi barci ma bama yi sabo da farin ciki kullun a kamar a mafarki muke ganin fadin filin Abuja a gaggauce muke muzo muga abinda zai gudana kai har gani muke yi ranar tana nesa kamar ba zata zo ba’’
Sai dai babban abin fata dai inji masu sharhi shine ayi taro lafiya kuma a wanye lafiya, yayin da Janar Muhammadu Buhari ke shirin fara aiki kuma kasar ke cikin tsaka mai wuya.