Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Tabbacin Ranar Da Buhari Zai Koma Najeriya


Shugaban Kasar Najeriya Mai Jiran Gado Muhammadu Buhari shi kadai a kofar fadar Firayim Ministan Britaniya.
Shugaban Kasar Najeriya Mai Jiran Gado Muhammadu Buhari shi kadai a kofar fadar Firayim Ministan Britaniya.

Litinin dinnan saura kwanaki 4 kacal a rantsar da sabon shugaban kasa a Najeriya, wato Janar Muhammadu Buhari mai ritaya. Amma baya cikin kasar, a dai-dai lokacin da take fuskantar karancin man fetur da wutar lantarki. Ko yaushe zai koma?

Darektan Kungiyar Masu Marawa Buhari Baya, Alhaji Ibrahim Abdulkarim ya tattauna da sashen Hausa na Muryar Amurka.

“Najeriya kasa ce dake hade da duniya, duk wani mataki da (Buhari) zai dauka na da tasiri ga ‘yan Najeriya da wadanda ba ‘yan Najeriya ba. Idan mutane suna tunanin za’a yi gyaran nan daga Najeriya ne, ai kaga ba zai yiwu ba”, a cewar Mr. Abdulkarim.

Darektan ya cigaba da cewa “yauzu ya wuce daukar shawara, tunda ya gana da jami’an gwamnati da dama”.

Sashen Hausa ya tambayi Ibrahim Abdulkarim ko mene ne dalilin rashin bayyana tafiyar Buharin zuwa Britaniya sai dai jin labari aka yi daga baya?

“Baza a bayyana ta ba, saboda ka san akwai masu gudu zasu gudu. Gwamma a barta a kwance, idan mun hadu da su ran 30 ga wata, zasu sani”, inji Abdulkarim.

A halin yanzu Najeriya na cikin matsalar rashin man fetur da wutar lantarki, kuma Buhari bai ce komai ba. Mr. Abdulkarim ya bada amsa.

“Shine shugaban kasa? Ku bari a rantsar da shi daga ran 29 ga wata”.

Da aka tambayi Darektan ko yaushe Buhari zai koma Najeriya, sai yace:

“In sha Allahu gobe ko jibi”.

Juma’ar da ta gabata ne zababben shugaban wanda ya taba yin mulkin soja na kama-karya ya sulale daga Najeriya ba tare da bayyanawa ba, kasa da mako guda a rantsar da shi ya kama bakin aiki. Wannan lamari dai ya zo a matsayin ba zata ga masu yi masa hidima da yawa, da magoya bayansa da ma ‘yan adawa.

Daga baya an fitar da hotunan shi tare da Firayim Ministan Britaniya David Cameron, sai dai babu tabbacin ranar da suka hadu. Ya zuwa yanzu ba’a ji ta bakin Buharin ba, wanda yake da halin baiwa ‘yan jarida damar tattaunawa da shi a duk inda yake. Litinin dinnan saura kwanaki hudu a rantsar da shi, amma yana can turai, baya Najeriya.

Masu hamayya na jam’iyyar PDP dake barin gado sun bayyana cewa ba dai-dai bane ya tafi kasar waje ba tare da sanar da jama’a ba, wadanda suka taru a Masallaci suna jiranshi domin yin addu’o’i. Bugu da kari, masu hamayya sun kara da cewa bai dace Buhari ya dogara da shawarwarin turawa ba biyo bayan sanarwar wakilansa masu cewa yaje neman shawarar hanyoyin tafiyar da kasa ne da Firayim Ministan Britaniya David Cameron, bayan haduwa da tsohon Firayim Minista Tony Blair.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG