Bello Galadanchi ya zanta da mataimakin shugaban kungiyar dillalan Man Fetur a Najeriya, Abubukar Maigandi Dakin Gari wanda ya tabbatar mana da cewa ma’aikatan NNPC sun koma bakin aikin su, kuma yanzu haka ana can an fara lodin Man Fetur da za’a rarraba a fadin kasar. Amma duk da haka man bai wadata ba a gidajen radiyo ba, kasancewar ana ‘dauko man ne daga kudancin Najeriya zuwa Arewacin kasar.
Idan har akwai wadataccen mai a kasa kamar yadda hukumar mai tayi ikirari, to baza’a dauki dogon lokaci ba kafin mai ya wadata a gidajen man Najeriya. Gwamnati ta nuna tanason a sayar da man fetur akan Naira tamanin da bakwai, amma matsalar da ake samu shine masu dakon man zuwa gidajen man sune ke sayar da man da tsada hakan ne ke sawa su kasa sayar da man da suke ‘dauke da shi akan farashin da gwamnati tace a sayar.
Abubukar Maigandi yace abin kunya ne ace irin kasar Najeriya ana wahalar mai, indai da gaskiya da rikon amana to babu dalilin da zai sa ace ‘yan Najeriya suna wahalar mai, mafita anan itace a gyara ma’aikatan tace man fetur wanda basa aiki a halin yanzu kamar yadda ya kamata, sai kuma a bai wa ‘yan kasuwa masu zaman kansu izinin gina nasu matatan man domin su zama kishiya ga ainishin kamfanonin matatan man fetur din da muke dasu a yanzu.