Matsalolin Da Aka Samu A Yayin Zaben 2023

Zaben 2023 a Najeriya

Zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka kammala a wannan shekarar ta 2023 ya hadu da tarin matsaloli da ke neman gyara kafin zaben gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki.

Zaben na 2023, an yi shi ne a lokacin da al’ummar Najeriya ke fama da rashin kudi saboda tsarin da gwamnatin tarayya ta fito da shi, na tabbatar da kaso mai yawa na kudin kasar sun koma banki, don ba gwamnati damar sa ido kan shiga da fitar kudade.

Wata matsala ita ce, ta karancin man fetur wadda watakila ita ta sanya kayan zabe basu isa rumfuna akan lokaci ba, lamarin da ya sa zaben ya kai dare ba a kammala ba kuma wasu ma basu sami damar yin zaben ba.

Malam Sani Yusuf, shugaban matasan unguwar Ali Kazaure a cikin birnin Jos, ya ce rashin kai kayan zabe a kan lokaci ya karya wa masu jefa kuri’a gwiwa, har sai da shugabanni suka rinka lallabarsu.

A wasu rumfunan kuwa na’urar da ke tantance masu kada kuri’a ce ta daina aiki, abin da ya sa mutane da dama basu jefa kuri’arsu ba, kamar yadda Yusuf Tanko ya bayyana.

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni a Najeriya, Barista Solomon Dalung, wanda ya yi takarar kujerar majalisar wakilai a zaben na bana, ya ce kamata yayi hukumar zabe ta gyara kurakurenta don maido da martabarta a idon ‘yan Najeriya.

A halin da ake ciki, al’ummar shiyyar Filato ta tsakiya sun nuna damuwarsu kan rashin fitar da sakamakon zaben Sanata kusan kwanaki goma bayan kammala zaben, inda aka sami takaddama tsakanin Diket Plang na jam’iyyar APC da Golkuna Gotom na jami’iyyar PDP, saboda dukkansu na ganin hukumar zabe ba ta yi musu adalci ba.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

Matsalolin Da Aka Samu Yayin Zaben 2023