Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar NNPP Ta Kwankwaso Ta Bi Sahun PDP Da LP Wajen Kiran A Soke Zabe


Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) ta bi sahun jam’iyyun PDP da na LP wajen kiran da a soke zaben shugaban kasa da na majalisun dokoki da a ka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Jam’iyyar ta yi wannan kiran ne a wata ganawa da manema labarai a ranar Talata, inda ta ce ya kamata a gudanar da sabon zabe cikin gaggawa.

Dole ne mu lura cewa, kowani irin hali ne kasarmu ke ciki, dole ne dukkan shugabannin su dauki zaman lafiya da tsaron kasa a matsayin mafi muhimmaci. Kasarmu ta fi kowane mutum girma kuma tabbas tana da mahimmanci fiye da duk wata bukata.

“Don ceto dimokaradiyya da kasarmu, ‘yan Najeriya da sauran abokanan Najeriya bai kamata su amince da wannan sakamakon zaben na yanzu ba. Don haka muna kira da a gaggauta dakatar da bayyana sakamakon zabe da kuma soke zaben shugaban kasa na 2023 a fadin kasar. Ya kamata a gudanar da sabon zabe cikin gaggawa,” in ji shugaban jam’iyyar na kasa Farfesa Rufa’i Alkali.

Jam’iyyar NNPP ta yi zarge-zarge da dama a kan hukumar zabe mai zaman kanta a kan yadda zaben ya gudana, ciki har da yadda hukumar INEC da gangan ta yi wa NNPP zagon kasa.”

Sauran dalilan da jam’iyyar NNPP ta bayar na bukatar soke zaben ga Hukumar INEC, sun hada da nuna takardun kada kuri’a da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi bayan ya kada kuri’a da kuma wasu wanda jam’iyyar ta yi zargin cewa wani salo ne na yakin neman zabe a ranar zabe.

Sun kuma yi korafin kan dakile wasu masu kada kuri’a da sayar kuri’a, gazawar na'urar BVAS da kada kuri'a da yawa, tashin hankali da kuma karyar da INEC ta yi kan ma'ajiyar bayanai ta iRev server.

Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Ifeanyi Okowa; da takwaransa na jam’iyyar Labour LP, Datti Baba Ahmed, a wata ganawa da manema labarai na hadin gwiwa da suka yi tun farko, sun yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta soke zaben ranar Asabar.

XS
SM
MD
LG