Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2023: Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta A Jahar Filato, Ta Bayyana Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Jahar


Zauren Gabatar Da Sakamakon Zabe
Zauren Gabatar Da Sakamakon Zabe

Farfesa Shehu Abdulrahman wanda ya sanar da sakamakon ya bayyana cewa jami’iyyar Leba ce ke kan gaba da kuri’u dubu dari hudu da sittin da shida da dari biyu da saba’in da biyu.

Sai jam'iyyar APC ke bi mata da kuri’u dubu dari uku da bakwai da dari daya da tasa’in da biyar.

Sai jam’iyyar PDP wace ta zo na uku da kuri’u dubu dari biyu da arba’in da uku da dari takwas da takwas.

Tun farko dai hukumomi a karamar hukumar Jos ta Arewa sun bayyana cewa an sami wata hatsaniya a wurin tattara kuri’u a karamar hukumar.

Shugaban karamar hukumar Jos ta Arewa, Shehu Bala Usman wanda ya tabbatar da hatsaniyar yace babu wanda ya sami rauni a rikicin.

Shehu Bala Usman ya bukaci wadanda basu gamsu da sakamakon zaben ba su bi matakin doka don samun adalci.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG