Matsalar Tsaro Da Ke Addabar Nijar Laifin Tsohon Shugaba Issoufou Ne - 'Yan adawa

Wannan shi ne karo na 3 da ‘yan bindiga ke karkashe fararen hula a kasa da wata 1 akan iyakar Nijar da Mali.

Yayin da hukumomi a Jamhuriyar Nijar suka ayyana shirin tsaurara matakai domin tunkarar matsalar tsaro da ta addabi jama’a a wasu yankunan kasar da ‘yan bindiga ke karkashe mutane ba gaira ba dalili ‘yan hamayya na kallon al’amari a matsayin gazawar gwamnatin tsohon shugaban kasa Issouhou Mahamadou.

Da yake jawabi a yayin ziyarar da suka kai a kauyen Gaigorou domin jajantawa jama’a abubuwan da suka faru a sakamakon harin ta’addancin da aka kai akan wasu fararen hula a yammacin asabar a kauyen na Gaigorou inda mutane 19 sukarasu, lokacin da suke bizne gawar wani dan uwansu Ministan tsaron kasar

Nijar Alkassoum Indatou ya ce duk da cewa wadanda suka yi wannan aika-aika suna ikirarin su Musulmai ne, ba za a kira su Musulmai ba.

Ya ce mutanen da ke ikirarin su musulmi ne kuma suna bugon gaban musulunci suke yiwa yaki su kashe mutane a lokacin da suka taru a makabartar musulmi domin jan’aizar gawar wani musulmi a cikin watan azumin Ramadan wadan da suka yi wannan ba za a kira su musulmi ba, kawai ‘yan bindiga ne da basu san abinda suke yi ba.

Ya ce kamar yadda Ministan cikin gida ya fada cewa za a dauki tsauraran matakai makamantan wadanda muka dauka a kwanakin baya a karkarar Anzourou.

Wannan shi ne karo na 3 da ‘yan bindiga ke karkashe fararen hula a kasa da wata 1 akan iyakar Nijar da Mali abinda ya sa Almansour Mohamed na kungiyar CAPAAN ke jan hankalin hukumomi game da girman matsalar tsaron da ake fuskanta a wannan yanki.

A wata sanarwar da suka fitar a jiya Lahadi jam’iyun adawa sun ayyana abin a matsayin wani bangare na koma bayan da gwamnatin tsohon shugaba Issoufou Mahamadou ta janyo wa kasar.

Sai dai kakakin jam’iyar PNDS Tarayya Asoumana Mahamdou ya ce babu kamshin gaskiya a wannan zargi.

Ko a daren Alhamis wayewar juma’ar da ta gabata wasu wadanda ake kyautata zaton mayakan Boko-Haram sun kai hari a garin Maine Soroa inda rahotanni suka ce sun yi awon gaba da motoci 6 na jami’an tsaro.

A ci gaba da karfafa matakan tsaro majalisar dokokin kasa a zamanta na yau ta yi na’am da bukatar tsawaita dokar ta baci a yankunan Tilabery da Diffa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Matsalar Tsaro Da Ke Addabar Nijar Laifin Tsohon Shugaba Issoufou Ne - 'Yan adawa