Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Daliban Makarantar Firamare 20 Da Suka Mutu A Gobarar Jamhuriyar Nijar

Yadda Na Samu Labarin Gobarar Da Ta Yi Sanadin Mutuwar 'Yata
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:41 0:00

Yadda na samu labarin gobarar da ta yi sanadin mutuwar 'yata.

A Jamhuriyar Nijar, an yi jana’izar daliban nan 20 da suka halaka a sanadiyar wata gobara da ta tashi a makarar firamarin unguwar Pays Bas da ke birnin Yamai. 

Da misalin hantsi ne aka yi jana'izar a makarbartar unguwar Sagata a birnin Yamai inda aka binne daliban makarantar firamarin Pays Bas wadanda suka rasu sakamakon wannan gobara.

Domin karrama wadanan yara an yiwa gawawwakinsu likkafani da turar Jamhuriyar Nijar.

Daruruwan mazaunan birnin Yamai da suka hada da iyaye da dangi da abokan zama ne suka fito don yi wa wadannan dalibai rakiya zuwa makwancinsu na karshe.

Jana’izar Daliban Makarantar Firamare 20 Da Suka Kone A Jamhuriyar Nijar
Jana’izar Daliban Makarantar Firamare 20 Da Suka Kone A Jamhuriyar Nijar

Kwanaki 3 bayan faruwar wannan mummunan al’amari, har yanzu wani mutun mai suna Boubacar Souley na tunawa da yadda ya tarar da gawar jikarsa kwance cikin burbushin wuta.

Bayan kammala aiyukan bizne wadanan dalibai an nufi makarantar da abin ya faru inda aka taru don yin addu’oi.

Karin bayani akan: Mohamed Bazoum, daliban, Nijar, da Nijer.

Kakakin gwamnati Minista Tidjani Abdouldari da ke daya daga cikin ministocin da shugaba Mohamed Bazoum ya aika a wurin wannan zama, ya ce gwamnati za ta tallafawa iyayen yaran da suka rasu a wannan gobara.

Jana’izar Daliban Makarantar Firamare 20 Da Suka Kone A Jamhuriyar Nijar
Jana’izar Daliban Makarantar Firamare 20 Da Suka Kone A Jamhuriyar Nijar

Sakataren kungiyar malaman makaranta ta SNEN Issouhou Arzika, ya sake jaddadawa hukumomi bukatar daukan matakan kiyaye sake aukuwar irin wannan tashin hankali.

Jana’izar Daliban Makarantar Firamare 20 Da Suka Kone A Jamhuriyar Nijar
Jana’izar Daliban Makarantar Firamare 20 Da Suka Kone A Jamhuriyar Nijar

A yammacin Talatar 13 ga watan Afrilu da ta gabata ne gobara ta tashi a makarantar fraimarin Pays Bas inda dakunan karatu na zana kimanin 27 suka kone kurmus lamarin da ya yi sanadin mutuwar dalibai galibinsu ‘yan kasa da shekaru 5 da haifuwa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

An Yi Jana’izar Daliban Makarantar Firamare 20 Da Suka Mutu A Gobarar Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

XS
SM
MD
LG