Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daruruwan 'Yan Najeriya Sun Gudu Nijar Bayan Harin Da Boko Haram Ta Kai Damasak


'Yan Gudun HIjira a Adamawa.
'Yan Gudun HIjira a Adamawa.

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ya yi tir da wannan hari tare da mika jajensa ga wadanda lamarin ya rutsa da su.

Rahotanni a Najeriya na cewa, dururuwan mutane daga garin Damasak da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, sun yi kaura zuwa Jamhuriyar Nijar, bayan wani hari da mayakan Boko Haram suka kai garin.

Garin Damasak wanda bai da nisa da kan iyakar Nijar, ya sha fama da hare-haren mayakan Boko Haram.

Wasu rahotanni sun ce mayakan kungiyar sun kai harin ne a ranar Laraba, kuma har mutum 10 sun mutu.

Titin karin Damasak
Titin karin Damasak

Shaidu sun fadawa kamfanin dillancin labarai na Rueters cewa, hare-haren sun kuma jikkata mutane da dama yayin da wasu suke makale a cikin dazuka.

Harin na ranar Laraba shi ne na biyar da mayakan suka kai wa garin a ‘yan makonnin nan.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, mayakan na Boko Haram har sun kafa tutarsu a garin bayan wannan hari.

Karin bayani akan: Damasak,​ Chibok, Boko Haram, Amnesty International, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaron kasar ba su ce uffan kan halin da ake ciki a garin na Damasak ba.

Garin ya taba fadawa hannun mayakan Boko Haram a karshen shekarar 2014 amma dakarun Najeriyar sun kwato shi a farkon shekarar 2015.

Yan Matan Chibok Sun Cika Shekara Bakwai

Hare-haren na zuwa a ranar da ragowar ‘yan mata daliban Chibok suka cika shekara bakwai a hannun mayakan, wadanda suka sace su a shekarar 2014.

Shugaba Muhammadu Buhari Da 'Yan Mata 82 Da 'Yan Boko Haram Suka Sako a 2017
Shugaba Muhammadu Buhari Da 'Yan Mata 82 Da 'Yan Boko Haram Suka Sako a 2017

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ta nuna takaicinta kan abin da ta kira gazawa da gwamnati ta yi, wajen kubutar da sauran daliban.

Amma fadar gwamnatin Najeriyar cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, ta ce, ‘yan matan na nan a ransu kuma tana iya bakin kokarin wajen ganin ta kubjutar da su.

Amurka Ta Yi Allah Wadai Da Harin

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ya yi tir da wannan hari tare da mika jajensa ga wadanda lamarin ya rutsa da su.

Amurkan har ila yau, ta nuna takaicinta kan yadda ake kai hari kan ma’aikan da ke ayyukan jin-kai.

“Ofishin Jakadancin Amurka na Allah wadai da harin da aka kai Damasak a jihar Borno. Kai hare-hare akan masu ayyukan agaji, hari ne akan bil adama. Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalai da wadanda wannan al’amari ya shafa a Najeriya.”

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG