Kamfanin dillancin labarai na ISIS da ake kira Amaq, yace dan kasar Syrian nan dake cikin 'yan gudun hijira, dan shekaru 27 da haihuwa, wanda ya tada nakiyoyi da suka hallakashi suka kuma jikkata wasu mutane 12 a Ansbach na kasar Jamus, "sojanta" ne.
Kamfanin dilancin labarai na Amaq, yace wata majiya cikin kungiyar, tace maharin "ya dauki matakin ne, a zaman amsa kiran da ISIS tayi cewa, mayakanta su auna kasashen da suke cikin rundunar taron dangi da suke yaki da kungiyar."
Wani babban jami'in tsaro a yankin Bavaria na kasar, ya gayawa manema labarai jiya Litinin cewa, maharin ya dauki sauti cikin woyar celula inda yayi mubaya'a ga shugaban ISIS Abu Bakr al-Baghdadi. Haka nan jami'in mai suna Joachhim Herman, yace an gano kayan hada-bam da sinadarai a gidan maharin.
Ministan kula da harkokin cikin gida na Jamus, Thomas de Maiziere, ya bada umarnin a karfafa matakan tsaro a tashoshin sifiri da wasu wurare.