Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Ta Takawa Kannywood Birki


Murtala Baharu Marubuci Fina Finai
Murtala Baharu Marubuci Fina Finai

Biyo bayan kiki kaka da kace-nace akan aikin gina katafaren birnin shirya fina finai a Kano (film village), gwamnatin tarayyar Nijeriya ta dakatar da kudirin wannan aiki.

Mai taimakawa shugaban kasa a fannin ayyukan majalisa Honarabul Abdurrahaman Kawu Sumaila ne ya tabbatar da dakatar da wannan aiki, yana mai cewar dama dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru da Bebeji Honarabul Abdulmumin Jibrin Kofa ne ya shigar da aikin cikin kasafin kudi.

Dangane da wannan batu ne muka samu zantawa da jamin hulda da jama’a na hadaddiyar kungiyar masu shirya fina-finai na Moppan Murtala Baharu Balarabe dangane da ra’ayoyinsa na soke wannan dandali.

Ya ce hannun daya bayar da hannun dama ne ya koma ya karbe da hannun hagu, kuma yakamata jama’a su nutsu su gano shin ita gwamnati ta daukar kudi ta saka a wurinda bata samun kudi.

Ya kara da cewa idan da ace mutane basu fito suna ta sukar wannan abin ba gwamnati da al’uma su zasu amfana kuma idan akayi wannan dandalin shirya fina finai, akalla mutane dubu arba’in da biyar zasu sami aikin yi.

Murtala Baharu Balarabe, yana mai cewa akalla mutane kimanin dubu talatin da bakwai (37,000) ne ke amfana kai tsaye ta dalilin fina finai a jihar Kano kawai, idan kuwa aka gina wannan dandali ai ba jihar Kano ba kasar baki daya zata amfana dama wasu kasar ketare kuma gwamnati zat sami kudaden shiga.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00

XS
SM
MD
LG