Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba Da Fafatawa A Gasar Kwallon Guragu Karo Na Farko A Najeriya


Kungiyoyin dake wakilatar jihohin Kano da Kaduna, da Katisna da jihar Filato, da Akawa Ibom, da Nasarawa da jihar Zamfara da Gombe ke fafatawa a wata gasa da ake gudanarwa karo na farko a fadin Najeriya, inda jihar Kano da Katsina da Nasarawa ke kan gaba a gasar wadda za’a kammala ranar 30 ga wannan watan da muke ciki.

Jimalar kwallaye 111 aka jefa a raga yayin da aka shiga rana ta shida da fara gasar ta kwallon guragu ta najeriya wadda ake yanzu haka ake gudanarwa a Kano, kuma kungiyoyi kimanin 10 ke fafatawa a gasar.

Alhaji Ahmad Abdullahi Libata, shine sakataren dake kula da wasannin guraru a Najeriya, ya ce a yanzu haka an buga wasanni kusan ashirin da biyar a cikin jihar Kano, kuma jihar Kano nada maki tara, jihar Katsina kuma nada maki takwas, sai kuma jihar Nasarawa da maki bakwai. Kano da Katsina ne zasu buga wasan karshe a ranar 30 ga watan Yuli.

Mataimakin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Ahmad Tudun wada ya ce akwai alamun jihar ta Kano zata lashe gasar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG