Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Karamar Hukuma Da Yafi Kanan Shekaru A Duniya!


Shugaban Karamar Hukuma Mr. Brandon Paulin
Shugaban Karamar Hukuma Mr. Brandon Paulin

Kusan za’a iya cewa Mr. Brandon Paulin, shine shugaban karamar hukuma mafi karancin shekaru a fadin duniya, a wannan zamanin karni na ashirin da daya 21. Kimanin shekara daya kenan da ta wuce, da aka zabi Mr. Paulin, a matsayin shugaban karamar hukumar Indian Head, karamar hukuma a jihar Maryland ta kasar Amurka.

A dai-dai shekarar da ya kammala karatun shina matakin sakandire yana mai shekaru goma sha takwas 18, aka zabe shi ya zama zababben shugaban karamar hukumar. Matashin dai yana shugabantar jama'a da yawan su, sama da dubu hudu, wadanda akwai tsofaffi masu shekaru da dama a cikin su, amma abun ban sha’awa duk wanda aka tambaya dangane da shugabancin shi sai dai suce Allah san barka.

Ya bayyanar da kan shi a matsayin yaro mai son ganin ya taimaka ma wasu, tun yana dan yaron shi, kuma yasamu sha’awar son shugabancin karamar hukumar su, tun yana dan makarantar firamari, ya gayama iyayen shi, cewar lallai sai yayi shugaban karamar hukumar su. Tun bayan shigar shi ofis, ya dau alwashin kawo kasuwanci da samar da hanyoyin kudin shiga ga karamar hukumar tashi.

Bayan shekara daya, ya bayyanar da irin cigaban da aka samu a karamar hukumar tashi karkashin jagorancin shi. Yayi amfani da yaruntar shi wajen jawo kamfanoni da ‘yan kasuwa don su zuba jari a karamar hukumar ta su, wanda hakan yayi nasara. Bai kuma dogara da kanshi kadai ba wajen gudanar da aiki, yakan nemi shawara daga wajen magabata, da suke da sanin rayuwa fiye da shi.

An dai bayyanar da Mr. Paulin, a matsayin matashi da yakamata ace kowane matsahi yayi koyi da irin zuciyar shi, da irin kokarin ganin ya bada tashi gudunmawa a wajen cigaban al’umar shi a ko ina a fadin duniya. Domin ta haka ne matasa zasu samu zuciyar da makamar sanin aiki tun da kuruciyar su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG