Jirgin sama kirar “Solar Impulse 2” wanda aka kirkira batare da yana amfani da ko digon mai ba, jirgin dai yana aiki da hasken rana ne wajen tashi da sauka. Shi dai wannan jirgin shine irin shi na farko da aka fara yi a fadin duniya. Shine kirar farko a cigaban kimiyya na karni na ashirin da daya.
Yanzu haka dai jirgin yana kan shawagin shi a karon farko, da yake zagaye duniya. Matukin jirgin Mr. Bertrand Piccard, sun tashi daga tashar jiragen sama a kasar Masar, ranar Lahadi, ana sa ran zasu sauka a kasar Abu Dhabi, bayan zagaye da suka gama na duniya yau Talata.
Matukin jirgin Piccard da ainihin wanda ya assasa tsarin jirgin Mr. Andre Borschberg, sun dau azama wajen gwada karko da iya karfin jirgin, tun a watan Mayu na shekarar 2015, suka fara tafiya inda suke kokarin zagaye duniya, inada suka fara da kasashen daular Larabawa, sukayi kewaye zuwa kowace nahiya.
A cewar matukin jirgin, lalai yawo a cikin jirgi irin wannan da baya amfani da mai, kuma shine kirar farko a duniya wani abun jin dadi ne, kuma idan har ana da bukatar magance matsalar dumaman yanayi, da magance matsalar zaman takewa, kana da magance duk wasu matsaloli da yanayi kan haifar to lallai sai an kokarta, wajen samar da irin wadannan abubuwan more rayuwa da basa da wasu illa ga rayuwar dan’adam da yanayi.