Matashi Mai Shekaru 28 Ya Hallaka Wata Mai Ciki Akan 50,000

A jiya ne wani matashi mai suna Ede Stephen Asuko daga jahar Uyo ya bayyana wa jami'an 'yan sandan jahar yadda wani mai unguwa a karkashin karamar hukumar Itu ya bashi aikin kawo masa gawar mace mai ciki.

Mujallar Vanguard ta wa llafa cewa 'yan sanda sun kama mutumin da ake zargin ranar 11 ga watan janairun da muke ciki tare da taimakon yayan sa da kuma 'yar uwar sa wadanda suka bukaci a sakaya sunan su, wadanda suka taimakawa jami'an tsaron da wasu bayanai har suka gano gawar matar a cikin gonar ayaba.

A yayin da aka tasa keyar wanda ake zargi da aikata laifin a shalkwatar 'yan sandan jahar dake Ikot-Akpanabia, mai magana da yawun 'yan sandan jahar Cordelia Nkwawe, ta bayyana cewa wanda ake zargin ya hallaka matar ne ya kuma boye gawar ta a gonar domin yin tsafi da gawar.

Mr Asuko ya bayyana wa manema labaru cewar mai unguwar kauyen su ne yasa shi aikata wannan aika aika. Ya kara da cewa su biyar mai unguwar ya biya kudi domin su samo masa gawar mace mai ciki, kuma ya bayyana cewa abinda ya kaishi wurin 'yan sandan shine domin ya bayyana masu abinda ya faru.

Daga karshe ya bayyana cewar wanda ya sa su aikin yayi masu alkawarin zai basu kudi dubu hamsin hamsin ne bayan sun kawo masa gawar, ya kuma kara vda cewa ko anini bai basu ba wanda hakanne ya harzuka daya daga cikin su har suka nemi tada rigima.