Yayin da Najeriya ke bikin cika shekaru hamsin da uku da samun 'yancin kai matasan Arewa Maso Gabashin kasar sun kalubali shugabancin kasar.
WASHINGTON, DC —
Yau Najeriya ke bikin cika shekaru hamsin da uku da samun 'yancin kai daga mulkin mallakar da Biritaniya ta yi mata.
Yayin da kasar Najeriya ke murnar cika shekaru hamsin da uku da samun 'yanci wasu 'yan kasar daga arewa maso gabas sun koka.Kungiyoyin matasa da wakilansu sun yi taro inda suka kalubali shugabanni kama daga kananan hukumomi zuwa ta jiha da majalisun tarayya da ma gwamnatin tarayya kanta domin irin halin da suka tsinci kansu a ciki.
Shugaban matasan arewa maso gabashin Najeriya Dauda Mohammed Gombe a jawabinsa ya ce suna fata daga wannan rana ta yau arewa maso gabas zata fara ganin canji. Ya ce a matsayinsu sun yiwa gwamnatin tarayya tambayoyi shida. Idan an basu amsoshin tambayoyin ya ce sun tabbata zasu kawo masu karshen matsalolin da suke ciki. Ga tambayoyin:
Shin wannan gwamnatin ta kasa ce baki daya ko ta wani bangaren Najeriya?
Wanene musabbabin wahalolin da talakawa da matasa suke ciki yau?
Wannan gwamnatin tana daukan arewa maso gabas a cikin bangaren Najeriya?
Wadanne irin manyan ayyuka wannan gwamnatin ta yi a arewa maso gabas?
Muna da wakilai a jamalisar tarayya da majalisar koli ta kasa?
Idan akwaisu wane irin aiki suka yiwa arewa maso gabas?
Daga amsarsu ga tambayoyin za'a san ko suna nan ko kuma babu su.
Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5