WASHINGTON, DC —
Gwamnatin jihar Yobe ta yi Allah wadarai da farmakin da wasu 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka kai a kan kolejin koyon aikin gona ta jihar dake Gujba, tana mai bayyana wannan harin a zaman ta'addanci, abin kyama.
Kakakin gwamna Ibrahim Gaidam na Jihar Yobe, Malam Abdullahi Bego, yace gwamnan ya kuma roki Allah da Ya tona asirin wadannan marasa imani da suka samu dalibai su na cikin barcinsu suka far musu su na karkashe su.
Abdullahi Bego yace duk wadanda suka kai wannan harin zasu gamu da fushin hukuma in sun shiga hannu, haka kuma tabbas su na rokon Allah da Ya hukumta wadannan marasa imanin dake kashe mutane babu gaira babu dalili, su na hana jama'ar kasa jin sakat a saboda bahaguwar manufarsu.
Yace su na kokarin ba jami'an tsaro irin hadin kan da suke bukata, kuma su na rokon jama'a da su ci gaba da bayyanawa hukumomin tsaro duk abinda suka gani bambarakwai domin a samu sukunin maganin wadannan 'yan ta'adda.
Gwamna Ibrahim Geidam ya kai ziyara asibitin Damaturu inda ya jajantawa wadanda suka ji rauni.
Ga tattaunawar da Abdullahi Bego yayi da Sahabo Imam Aliyu...