WASHINGTON, DC —
Najeriya ta cika shekaru hamsin da uku da samun 'yancin kai a tsakiyar tabarbarewar al'amuran tsaro musamman ma a arewacin kasar inda duk safiya sai an ji labarin kisan bayin Allah a wani yanki. Kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta ne ma ya hana gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan shirya gagarumin shagali albarkacin cikon shekarun hamsin da ukun na zaman mulkin kai. Daya daga cikin wakilan Sashen Hausa a Abuja, Nasiru Adamu el-Hikaya ya hada wannan rahoto na tuna baya da kuma duba halin da ake ciki.
Daga samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka ya zuwa yanzu kasar Najeriya ta ga sauyin al'amura iri-iri