Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakamakon Zargin Kisan Gilla A Abuja, Minista bala Mohammed Ya Bayyana A Majalisa


'Yan sandan kwantar da tarzoma na Najeriya su na sintiri
'Yan sandan kwantar da tarzoma na Najeriya su na sintiri

Ministan raya birnin tarayya Abuja Bala Mohammed ya bayyana gaban kwamitoci biyu domin amsa tambayoyi kan zargin kisan gilla a Abuja.

Kwamitoci biyu na majalisar tarayyar Najeriya sun karbi shaida daga ministan raya birnin Abuja Malam Bala Abdulkadiri Mohammed, dangane da zargin kisan gilla da ake yiwa jami'an tsaro bayan mataki da suka dauka makon jiya d a ya kai ga kisan akalla yanzu mutane 9-10 a unuguwar gidajen 'yan majalisa da ake kira Apo Village da turanci.

Senata Bala Mohammed ya gayawa kwamitocin biyu na kula da lafiyar d a kadarorin jama'a da kuma kwamitin tsaro cewa gidan nan da jami'an tsaro suka kai somame akai ta wata mace ce da ake kira Adone Oluwole Salisu, kuma ba soja bace.

Senatan ya kara da cewa jami'an tsaro basu shaida ma'aikatar raya birnin Abuja ba kamin su dauki wannan mataki saboda suna da hurumin yin haka, amma daga bisani sun gayawa ma'aikatar abunda ya faru, kuma hukumarsa ta gamsu.

Haka shima babban hafsan hafsoshin Najeriya Janar Ehijerika yayi bayani cewa har da sojoji cikin jami'an tsaro da suka kai farmaki kan gidan. Kamar yadda za'a ji karin bayani daga wakiliyarmu Madina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Shiga Kai Tsaye
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG