WASHINGTON, DC —
Albarkacin cikon shekaru hamsin da uku da samun 'yancin kan kasar Najeriya Halima Djimrao ta tattauna da Lauya Aminu Hassan Gamawa na jami'ar Harvard ta nan Amurka, inda ya duba al'amarin kasar Najeriya daga wancan lokaci ya zuwa yanzu ya ce ci gaban da aka samu bai amfani talakan kasar Najeriyar ba. Lauya Aminu Hassan Gamawa ya fara da bayyana mahimmacin samun 'yancin kai ga kowace kasa da kuma kowace al'umma, amma ya ce su dai 'yan kasar Najeriya ba su da wani kwakkwaran dalilin yin murnar cikon shekaru hamsin da uku da samun 'yancin kai.
Aminu Hassan Gamawa yace yanzu ba mulkin mallaka ake yi ba, amma duk manufofin shugabannin kasar domin su dad'ad'awa turawa ne