Wasu matasa masu yin aiki a karkashin shirin tallafin rarar man fetur na SURE-P, da yawan su yan kai dubu daya da dari biyar sun shiga cikin halin tangaririya a jihar Neja.
Matasan sun ce a halin yanzu basu san makomar su ba domin kuwa yanzu watani bakwai Kenan ba’a biya su albashi ba a jihar Neja, duk kuwa da suna gudanar da aikin da aka sasu a karkashin shirin na SURE-P.
Dama dai tsohuwar Gwamnatin da ta gabata ne ta dauke su aiki, suna gudanar da aiyuka daban daban, kamar duba gari da kula da cunkoson ababen hawa akan titi, da kuma kula da gandun daji.
Amma a yanzu matasan sun ce an barsu suna tangaririya hanu rabana, Isa Abubakar Vatsa, shugaban tawagar matasan yace “ A kowane wata yakamata su dinga bamu dubu goma sha biyar biyar ne kowane mutun daya, tunda muka fara aiki ranar 1, ga watan Yuni 2013, har zuwa watan Oktoba, 2014, suka dakatar da biyan mu.”
Gwamnatin jihar Neja, dai tace ta san da wannan matsala, amma gaskiyar lamari shine suna fama da talauci, inji sakataren yada labarai na Gwamnan jihar Dr. Ibrahim Doba, ya kara da cewar "´Idan SURE-P, suka turo kudi sai mu biya su ia’ ko tunda bashi ne suke bin Gwamnati."