WASHINGTON, DC —
Manoma a jihar Adamawa, sun koka a bisa tafiyar hawainiyar da aikin madatsar ruwan Coci, ke fuskanta wanda aka faro tun zamanin tsohowar hukumar PTF.
Shine dai wannan aikin madatsar ruwan na cikin manyan aiyukan da hukumar ta PTF, ta barwa gwamnatin Olusegun Obasanjo, a shekarar 1999, amma kawo yanzu aikin na nan kamar jiya.
Manufar aikin dai shine inganta aikin noma domin samarda abinci da kuma rage ambaliyan wura dake addabar fadar jihar ta Adamawa, da kuma samar da aikin yi ga din bin manoman da zasu rugumi noman rani.
Wani masani aikin noma Mr. Joseph Jario, shima ya koka da yadda aikin ke tafiya hawainiya, yace idan aka kamala wannan madatsar ruwan tabbaci hakika, jama’a da dama zasu samu aikin yi.